Yanzu yanzu nake samun labari cewa
Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; Zamantakewar aure, Rayuwar yau da kullum Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da matsalolin da ke afkuwa bayan raba gida da maigida ya yi, a yayin da ya ke yunkurin karo abokiyar zama (Kishiya), da kuma amfanin da ke tare da hakan.
Da yawan wasu matan na zabar raba gida a yayin da miji zai karo abokiyar zama, ta gefe guda kuma akan samu wadanda ba sa son a raba musu gida, wanda dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko mene ne amfanin rabawar da kuma rashin rabawar? Wadanne irin matsaloli kowanne bangare zai iya haifarwa? Ta wacce hanya ya kamata a magance afkuwar hakan?Ga kuma ra’ayoyin nasu kamar haka
Amfanin rabawa shi ne; samun saukin kishi. Rashin rabawa kuma yana kawo matsaloli da yawa musamman inba a shiri, amman in anbraba kowa da gidanshi kuwa, indai ba a sha’anin danginshi ko wata matsala ba babu me ganin juna sai dai in miji a tsaye yake a gidanshi, in kuwa an fi karfinshi a gida kuwa to inba bikin ‘family’ din miji ba babu inda za a hadu. Ina tunanin babu wata hanyar daya kamata a magance irin wannan matsalar face ta hanyar mijin, shi ne kadai zai iya magance matsalar gidanshi har in ba mijin hajiya bane shi. Shawara ga uwargida shi ne; tayi hakuri, namiji mijin mace hudune ba a haifa mata ita kadai ba, kila ma gidansu ba mamanta kadai ba, ita kuma amarya tabi uwargida koda ba gida daya suke ba, ina ganin shi ne zaman. Don kuwa babu wanda zai iya korar wani cikinsu, kuma kowa ana so aka aureta Allah ya sa mu dace ya rage mana zafin kishi.


0 Comments