Yanzu yanzu nake samun labari cewa
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci jama’ar Jihar Adamawa da su goyi bayan gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kyawawan ayyukan ci gaban da gwamnan ke gudanarwa.
Atiku, wanda shi ne dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya yi kiran ne ranar Litinin a Yola.
Ya ci gaba da cewa “Fintiri ya yi abin a zo agani a yaba, musamman ta bangaren ayyukan ci gaba, ilimi da bangaren kiwon lafiya.
“Na yaba wa gwamnatin da irin kyakkyawan nasarorin da ta cimma, musamman ta fuskacin ayyukan ci gaba, ilimi da kiwon lafiya” in ji Atiku.
Wannan ita ce ziyarar tsohon mataimakin shugaban kasar a jihar, tun bayan gudanar da babban zaben 2023, da ya samu tarba daga mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta.


0 Comments