Akalla wasu ‘yan gudun hijira uku ne suka rasu sannan sama da gidaje 1000 suka kone bayan da gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar Laraba kuma ta dauki sama da awa daya kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta.
Babban Darakta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad Sa’idu ne, ya bayyana hakan a Maiduguri ga manema labarai.
Ya ce jami’an sa-kai na CJTF, da jami’an tsaro da ‘yan gudun hijira, sun taimaka wajen kashe gobarar.
Tuni dai gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum ya kafa kwamiti don gudanar da binciken musababbin tashin gobarar.


0 Comments