Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kotu Ta Bayar Da Belin Tsohon Shugaban Hukumar KASCO Kan Miliyan 500



 Yanzu yanzu nake samun labari cewa

Wata babbar kotua Jihar Kano ta belin tsohon Manajan Darakta na KASCO kan kudi miliyan 500.


Leadership ta ruwaito cewa ana tuhumar tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Noma na Jihar Kano, KASCO, Bala Inuwa Muhammad da karkatar da sama da Naira Biliyan hudu.


Ofishin babban mai shari’a na jihar ne, ya shigar da karar, biyo bayan binciken da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa (PCACC) ta gudanar.


PCACC ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa wanda ake tuhumar tare da wanu sun karkatar da sama da Naira biliyan hudu daga asusun kamfanin.


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi zargin cewa, Mista Muhammed da dansa, Bala Muhammed da wasu mutane biyu sun karkatar da sama da Naira biliyan hudu na kudaden gwamnatin jihar.

Post a Comment

0 Comments