Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

INEC Ta Bada Umarnin Sake Zabe A Wasu Sassan Jihar Kogi

 Yanzu yanzu nake samun labari 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu unguwannj a Jihar Kogi sakamakon wasu kura-kurai da aka samu.

Jihar Kogi dai na daya daga cikin jihohi uku da aka gudanar da zabukan gwamnoni a ranar Asabar.


Biyo bayan wasu takardun sakamakon zabe da aka yada a kafafen sada zumunta a yayin da ake kan gudanar da kada kuri’a, sabida haka, INEC ta dakatar da zabukan a unguwanni tara, za a fitar da cikakken bayani bayan kammala bincike.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mohammed Haruna, kwamishinan zabe na jihar, ya ce, za a sake gudanar da sabon zabe a yankunan da lamarin ya shafa.



Post a Comment

0 Comments