Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Majalisar Ɗinkin Duniya Da Tarayyar Turai Sun Miƙa Cibiyar Kula Da Matan Da Aka Ci Zarafinsu Ga Sokoto

 

Yanzu yanzu nake samun labari


Yayin da aka kammala aikin shirin kawo karshen cin zarafin mata na Kungiyar Tarayya Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya tare da mikawa ga masu ruwa da tsaki, Gwamnan Jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa bisa tallafin shirin, gwamnatin jihar ta inganta kula da wadanda suka tsira daga Cin Zarafi na Jinsi (SGBV) a cikin jihar.


“Mun inganta ayyukan kula da waɗanda suka tsira daga cin zarafi na Jima’i saboda bambancin jinsi (SGBV) kuma mun tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun sami damar samun kulawar da suke buƙata don sake gina rayuwarsu.” Ya bayyana hakan ne a wajen taron kammala shirin tare da mika cibiyar da aka samar ga Gwamnatin Jihar Sokoto, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, a dakin taro na kasa da kasa da ke Sokoto.


“Mun inganta ayyukan kula da waɗanda suka tsira daga cin zarafi na Jima’i saboda bambancin jinsi (SGBV) kuma mun tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun sami damar samun kulawar da suke buƙata don sake gina rayuwarsu.” Ya bayyana hakan ne a wajen taron kammala shirin tare da mika cibiyar da aka samar ga Gwamnatin Jihar Sokoto, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, a dakin taro na kasa da kasa .

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Aliyu Dikko, ya jaddada cewa “jihar ta yi namijin kokari wajen tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun samu kulawar da ta dace, tare da saukaka yunkurin farfadowa don sake gina rayuwarsu bayan da suka tsallaka siradi.

Ya nanata kudurin jihar na kawar da cin zarafi da munanan ayyuka da ake yi wa mata da ‘yan mata, ya kuma jaddada gagarumin ci gaban da aka samu ta hanyar shirin mai lakabin ‘Spotlight Initiative’, wanda ya kasance wani cikakken shiri da aka tsara don tabbatar da cewa kowace mace walau babba ko yarinya za ta iya rayuwa a Jihar Sokoto ba tare da fuskantar wani tashin hankali da abubuwa na cin zarafi ba.

“Gwamnati ta himmatu wajen samar da dokoki da tsare-tsare da za su kare mata da ‘yan mata, tare da samar da yanayin da zai tabbatar da yin hukunci da adalci ga wadanda suka tsira daga cin zarafin mata a Jihar Sakkwato.” Ya bayyana.

Post a Comment

0 Comments