Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Bai Kammala Ba


 

Yanzu yanzu nake samun labari cewa 

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Sai dai jam’iyyar APC, ta kalubalanci nasarar Lawal, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP.


Kotun sauraren kararrakin zabe ta amince da zaben Lawal, amma APC ta garzaya kotun daukaka kara.


A ranar Alhamis ne wani kwamitin alkalai uku ya soke nasarar Lawal tare da bayar da umarnin sake gudanar da zaben a kananan hukumomi uku.


Post a Comment

0 Comments