Kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta bayar da wasu sharudan belin Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado bisa zargin almundahana.
Alkalin kotun, Mai shari’a Danladi Umar, ya bayar da sharudan a ranar Alhamis, lokacin da Muhuyi ya gurfana a gaban kotun.
Sharudann belin sun hada da biyan Naira miliyan biyar tare da gabatar mutane biyu da za su tsaya masa, sannan su kasance suna aiki a birnin tarayya, Abuja.
Bugu da kari, wadanda za su tsaya masa dole su ajiye hotunansu guda biyu a kotun, domin neman amfani da su a matsayin wasu matakai na cika sharudan.
Ana zargin Muhuyi da kin bayyana kadarorinsa wanda yana daga cikin dokokin ma’aikata kafin karbar duk wani mukami.


0 Comments